Skip to main content

DATTAWAN AREWA NA BUKATAR BUHARI DA YA YI MURABUS

 Kungiyar dattawan arewa ta tsaya kan bakarta na neman Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi murabus - Kungiyar ta ce hujjojin da ke kasa sun isa su nuna cewa kiran da tayi daidai ne - Kakakin kungiyar, Hakeem Baba Ahmed, ya ce Shugaban kasar ya gaza kare yan Najeriya Kungiyar dattawan arewa ta sake sabonta kiran da take yi na neman Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi murabus. Da yake magana a yayin hira da Channels Television a ranar Laraba, 2 ga watan Disamba, kakakin kungiyar, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce hujjojin da ke kasa sun marawa kiraye-kiraye da suke yi ga Shugaban kasar yayi murabus a baya. Dattawan arewa na nan akan bakarsu na neman Buhari ya sauka, In ji Hakeem Baba Ahmed Hoto:“Hujjar da ke kasa ya marawa abunda muke fadi baya. Shugaban kasar ya yi rantsuwa da Al-Qur’ani don kare al’umman kasar. Ya gaza yin hakan. “Wannan shine shekararsa ta biyar a kan mulki. Halin da ake ciki yana kara tabarbarewa a karkashinsa kuma babu alama da ke nuna abubuwa za su inganta.” Da farko mun kawo cewa a ranar Talata, 1 ga watan Disamba, an bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi murabus daga kujerar mulki biyo bayan hare-hare da hauhawan rashin tsaro a kasar, tare da alamu da ke nuna gwamnatin ta rasa abun yi. Kungiyar dattawa arewa (NEF) ce ta gabatar da wannan bukata inda ta caccaki fadar shugaban kasa a kan rashin tunani game da hare-haren da aka kaiwa yan Najeriya da ke zama a yankunan karkara. Bayan kisan Zabarmari, dakarun soji sun kaddamar da hari kan shugabannin Boko Haram a dajin Sambisa (bidiyo) Kungiyar tace rayuwa a karkashin wannan gwamnati bata da wani tasiri. Ta kuma bayyana cewa abunda ake bukata da shugaba da ya rasa mafita shine yayi murabus. 

Comments

Popular

IDAN BAKA MUTU BA,TO BA KA KARE GANIN ABUBUWA BA

 Wata Mata mai zaman kanta ta sayar da Danta mai kimanin watanni  hudu akan naira dubu dari ukku. Matar mai suna  Zainab Adamu 'yar asalin jihar Adamawa mazauniya Kofar Kaura da ke Katsina,ta hada baki da kawarta mai suna Ruth Kenneth, inda suka sayar wa wata mai suna Chidinma Omehyar shekaru 43 daga jihar Anambra danta akan Naira 300,000.