Skip to main content

Posts

DATTAWAN AREWA NA BUKATAR BUHARI DA YA YI MURABUS

  Kungiyar dattawan arewa ta tsaya kan bakarta na neman Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi murabus - Kungiyar ta ce hujjojin da ke kasa sun isa su nuna cewa kiran da tayi daidai ne - Kakakin kungiyar, Hakeem Baba Ahmed, ya ce Shugaban kasar ya gaza kare yan Najeriya Kungiyar dattawan arewa ta sake sabonta kiran da take yi na neman Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi murabus. Da yake magana a yayin hira da Channels Television a ranar Laraba, 2 ga watan Disamba, kakakin kungiyar, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce hujjojin da ke kasa sun marawa kiraye-kiraye da suke yi ga Shugaban kasar yayi murabus a baya.  Dattawan arewa na nan akan bakarsu na neman Buhari ya sauka, In ji Hakeem Baba Ahmed Hoto:“Hujjar da ke kasa ya marawa abunda muke fadi baya. Shugaban kasar ya yi rantsuwa da Al-Qur’ani don kare al’umman kasar. Ya gaza yin hakan. “Wannan shine shekararsa ta biyar a kan mulki. Halin da ake ciki yana kara tabarbarewa a karkashinsa kuma babu alama da ke nuna abubuwa za su inganta.” Da f...
Recent posts

IDAN BAKA MUTU BA,TO BA KA KARE GANIN ABUBUWA BA

 Wata Mata mai zaman kanta ta sayar da Danta mai kimanin watanni  hudu akan naira dubu dari ukku. Matar mai suna  Zainab Adamu 'yar asalin jihar Adamawa mazauniya Kofar Kaura da ke Katsina,ta hada baki da kawarta mai suna Ruth Kenneth, inda suka sayar wa wata mai suna Chidinma Omehyar shekaru 43 daga jihar Anambra danta akan Naira 300,000.